Friday, November 16, 2012

Gizago Ba Ka Da Sabo

Kungiyar Gizago dai kungiya ce ta zumunci wadda kadan daga cikin manufofinta suka hada da sadar da zumunci tsakanin membobi da kuma farfado tare da inganta al'adun Hausa. 'Yan kungiyar kan fadakar tare da yiwa juna nasiha kan al'amuran rayuwa. Haka kuma sukan taya juna murna ko jaje a yayin da wani abin farin ciki ko akasin hakan ya sami daya daga cikinsu. Suna kokarin farfado da kyawawan al'adun Hausa da ko dai suka bace gaba daya ko kuma wasu bakin al'adun ke neman dusashesu.

Kalmar Gizago dai a Hausance tana nufin wani abin da masassaki ke amfani da shi wajen gudanar da aikinsa na sassaka. Akan yi karin magana da kalmar cewa 'Gizago ba ka da sabo'. Wato duk yadda masassakin nan ya dade yana amfani da gizagonshi, ba zai hana gizagon nan sarar hannun masassakin nan ba in bai sanya kula gami da taka-tsantsan ba.

Ma'anar wannan kalmar a kungiyance kuwa tana nufin tsage gaskiya da yiwa juna nasiha in har dan kungiyar ya yi ba daidai ba, ba tare da la'akari da sabo ba. A kodayaushe dai kokarin 'yan kungiyar shine yadda za a yaukaka dankon zumunci tsakanin juna.

Kungiyar Gizago ta yi taronta na farko ne inda 'yan kungiyar suka sami damar ganin juna ido-da-ido a lokacin da suka tattaru a Kanon Dabo a ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2009. Tun daga wannan lokacin dai lamurran kungiyar sai kara habaka suke, zumunci na kara danko domin kuwa har auratayya ta gudana tsakanin wasu daga cikin membobin kungiyar.

Thursday, November 8, 2012

Sokoto 2012

Yanzu haka dai shiri yayi nisa game da taron Gizago a Garin Sokoto cikin watan December. Bayanan da muke samu daga shugaban kungiyar reshan Jihar Sokoto M.A.Faruk yace shiri yayi nisa domin gudanar da taron kuma ya shaida mana cewa nan bada dadewa ba zasu bayar da sanarwa ta karshe dan gane da taron.

Friday, September 24, 2010

Gizagawa mata na kokarin kulla zumunci

Wani bangare na matan da suka sami halartar taron Kano

Bello BG da Danmasani a taron Kaduna

Dakta Bala Muhammad na nashi jawabin a taron Kano

Monday, September 20, 2010

Shugaban Gizago na Kano, Nura Adamu Ahmed ke karbar kyauta a madadin uban kungiya na kasa, Dr. Yusu Adamu a taron Kano

Mallam Musa Yobe daga Ibadan a taron Kano

Mallam Auwal Ibadan a taron Kano

Wasu Gizagawan zumunci a taron Kaduna

Ziyarar Gizagawan Kaduna zuwa gidajen marayu da nakasassu

A ranar Lahadi, 5 ga watan Satumba ne Gizagawan Kaduna su ka niki gari
don kai ziyara gami da agaji ga gidajen marayu da nakasassu da ke
Zaria. Ziyarar dai ta sami nasara kwarai da gaske wadda ta gudana
karkashin jagorancin shugaban Gizago na jihar, Mallam Zakariyya Sa'eed
Mai Gwanjo.
Gidan Rainon Marayu gizagawan su ka fara yi wa tsinke inda aka yi musu
cikakken bayanin yadda ake tafiyar da kulawa da wadannan yara, tare
kuma da karin haske a kan yadda  ake samun su inda jami'an gidan suka
bayyana cewa wasu daga cikin yaran akan tsince su ne tun suna kanana a
kwararo-kwararo bayan an wurgar da su, yayin da wasu kuma 'yan matan
da su ka haife su ba tare da aure ba kuma ba su son wurgar da su, su
kan kawo su nan gidan don kulawa da su.
A karshen ziyarar dai an mika kayayyakin tallafi da su ka hada da
kayayyakin abinci da suturu don agazawa wadannan yara.
Haka kuma ziyarar ta kasance a Gidan Kula Da Nakasassu da ke
makwabtaka da na marayun duk dai a birnin na Zazzau inda jami'ai suka
kewaya da Gizagawan su ka nuna musu halin da wadannan nakasassu ke
ciki. A wannan gida ne aka nuna wa Gizagawan wani bawan Allah da
sojoji su ka kawo shi gidan tun lokacin yakin basasar kasar nan bayan
da bom ya tashi dab da shi har ya yi sanadiyyar kurumta shi. A wannan
gida kam akwai abubuwan ban tausayi da dama wadanda ka iya sanya mutum
zub da hawaye.
Nan ma dai kamar Gidan Marayu, an mika kayayyakin abinci da suturu da
sauran ababen agaji.

YM Rigasa a Gidan Murtala, Kano inda taron Kanon ya gudana

Shugabar mata ta Gizago, Hajiya A'isha Tarauni a taron Kaduna

Kadan daga cikin matan da suka halarci taron Kaduna

Auwal Suleja, Yunusa Nassarawa da Mallam Auwal Ibadan a taron Kaduna

Wani bangare na Gizagawa a taron Kaduna

Ado Ahmad Gidan Dabino a taron Kaduna

Shahararren marubuci, Ado Ahmad Gidan Dabino a lokacin taron Kano

Masu saurauta ma ba a bar su a baya ba wajen kulla zumunci a Gizago

Friday, August 27, 2010

Daya daga cikin iyayen Kungiyar Gizago na Kasa, Ado Saleh Kankia ya albarkaci taron Gizagon a Kaduna.

Shugaban Kungiyar Muryar Talaka na Kasa, Bagizage Zaidu Bala tare da Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano, Bagizage Yasir Ramadan Gwale a lokacin taron Gizago a Kaduna cikin watan Afrilun 2010.

Zaidu Bala da Yasir Ramadan Gwale 

Tsohon Shugaban Gizago na Jihar Kaduna, Idris Ibrahim Kubau yana gabatar da na shi jawabin lokacin taron Kano.

Nan kuma Sheikh Aminu Daurawa ne a taron Kano

Manyan malamanmu ma sun albarkaci tarukanmu. Nan Sheikh Tukur Al-Mannar ne a taron Kaduna.

YM Rigasa tare da Ado Ahmad Gidan Dabino a Birnin Dabo

Dr. Bala Muhammad ya daidaita sahun Gizagawa a Birnin Dabo

Mata adon gari, su ma ba a bar su a baya ba a taron Gizago da ya gudana a Kano Birnin Dabo

Kaka-Tsara-Kaka: Ga Gizago, ga Dodo sun game a lokacin taron Kano

Ibrahim Mai Hoto, Abubakar Abdurrahman, YM Rigasa, Bashir Yahuza da kuma wani Bagizagen a lokacin taron Gizago na Kano.

Bello BG Gidan Madi da YM Rigasa lokacin taron Kaduna a watan Afrilun 2010

Shugaban Gizago na Kasa, Muntaka Abdulhadi Dabo

Jamila Complete Sokoto tana tattaunawa da 'yan jaridu a lokacin taron Gizago na kasa da aka yi a garin Kaduna a watan Afrilun 2010.