Friday, November 16, 2012

Gizago Ba Ka Da Sabo

Kungiyar Gizago dai kungiya ce ta zumunci wadda kadan daga cikin manufofinta suka hada da sadar da zumunci tsakanin membobi da kuma farfado tare da inganta al'adun Hausa. 'Yan kungiyar kan fadakar tare da yiwa juna nasiha kan al'amuran rayuwa. Haka kuma sukan taya juna murna ko jaje a yayin da wani abin farin ciki ko akasin hakan ya sami daya daga cikinsu. Suna kokarin farfado da kyawawan al'adun Hausa da ko dai suka bace gaba daya ko kuma wasu bakin al'adun ke neman dusashesu.

Kalmar Gizago dai a Hausance tana nufin wani abin da masassaki ke amfani da shi wajen gudanar da aikinsa na sassaka. Akan yi karin magana da kalmar cewa 'Gizago ba ka da sabo'. Wato duk yadda masassakin nan ya dade yana amfani da gizagonshi, ba zai hana gizagon nan sarar hannun masassakin nan ba in bai sanya kula gami da taka-tsantsan ba.

Ma'anar wannan kalmar a kungiyance kuwa tana nufin tsage gaskiya da yiwa juna nasiha in har dan kungiyar ya yi ba daidai ba, ba tare da la'akari da sabo ba. A kodayaushe dai kokarin 'yan kungiyar shine yadda za a yaukaka dankon zumunci tsakanin juna.

Kungiyar Gizago ta yi taronta na farko ne inda 'yan kungiyar suka sami damar ganin juna ido-da-ido a lokacin da suka tattaru a Kanon Dabo a ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2009. Tun daga wannan lokacin dai lamurran kungiyar sai kara habaka suke, zumunci na kara danko domin kuwa har auratayya ta gudana tsakanin wasu daga cikin membobin kungiyar.

Thursday, November 8, 2012

Sokoto 2012

Yanzu haka dai shiri yayi nisa game da taron Gizago a Garin Sokoto cikin watan December. Bayanan da muke samu daga shugaban kungiyar reshan Jihar Sokoto M.A.Faruk yace shiri yayi nisa domin gudanar da taron kuma ya shaida mana cewa nan bada dadewa ba zasu bayar da sanarwa ta karshe dan gane da taron.