Monday, September 20, 2010

Ziyarar Gizagawan Kaduna zuwa gidajen marayu da nakasassu

A ranar Lahadi, 5 ga watan Satumba ne Gizagawan Kaduna su ka niki gari
don kai ziyara gami da agaji ga gidajen marayu da nakasassu da ke
Zaria. Ziyarar dai ta sami nasara kwarai da gaske wadda ta gudana
karkashin jagorancin shugaban Gizago na jihar, Mallam Zakariyya Sa'eed
Mai Gwanjo.
Gidan Rainon Marayu gizagawan su ka fara yi wa tsinke inda aka yi musu
cikakken bayanin yadda ake tafiyar da kulawa da wadannan yara, tare
kuma da karin haske a kan yadda  ake samun su inda jami'an gidan suka
bayyana cewa wasu daga cikin yaran akan tsince su ne tun suna kanana a
kwararo-kwararo bayan an wurgar da su, yayin da wasu kuma 'yan matan
da su ka haife su ba tare da aure ba kuma ba su son wurgar da su, su
kan kawo su nan gidan don kulawa da su.
A karshen ziyarar dai an mika kayayyakin tallafi da su ka hada da
kayayyakin abinci da suturu don agazawa wadannan yara.
Haka kuma ziyarar ta kasance a Gidan Kula Da Nakasassu da ke
makwabtaka da na marayun duk dai a birnin na Zazzau inda jami'ai suka
kewaya da Gizagawan su ka nuna musu halin da wadannan nakasassu ke
ciki. A wannan gida ne aka nuna wa Gizagawan wani bawan Allah da
sojoji su ka kawo shi gidan tun lokacin yakin basasar kasar nan bayan
da bom ya tashi dab da shi har ya yi sanadiyyar kurumta shi. A wannan
gida kam akwai abubuwan ban tausayi da dama wadanda ka iya sanya mutum
zub da hawaye.
Nan ma dai kamar Gidan Marayu, an mika kayayyakin abinci da suturu da
sauran ababen agaji.

No comments:

Post a Comment